Sakamakon farko na zaben, ya nuna cewa, shugaba Uhuru Kenyatta ya samu kuri'u miliyan 7.77 kimanin kaso 54 cikin 100, yayin da abokin takararsa Raila Odinga ya samu kuri'u miliyan 6.39, kimanin kaso 44 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.
A cewar jagoran adawar, wasu masu kutse da ba a san ko su wane ne ba, sun yiwa na'urar tattara sakamakon hukumar zaben kasar kutse, domin hana shi lashe zaben shugabancin kasar na jiya Talata. (Ibrahim)