Msando dai yana daga cikin manyan jami'an hukumar zaben kasar wadanda ke rike da lambobin asiri na na'urori masu kwakwalwa na hukumar da kuma yadda ake adana sakamakon zaben kasar.
A ranar Litinin ne ake tabbatar da mutuwar jami'in, 'yan sa'o'i kafin ya tashi zuwa kasashen waje domin gwajin na'urorin bayyana sakamakon zaben kasar kai tsaye.
A ranar Asabar din da ta gabata ce aka samu gawarsa da ta wani dalibi dan shekaru 21 da haihuwa wanda ke karatun ilimin abinci mai gina jiki a cikin daji a wajen birnin Nairobi, fadar mulkin kasar. (Ibrahim Yaya)