in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COMESA ta yi hasashen za'a yi zabe cikin lumana a Kenya
2017-08-07 09:07:22 cri
Babbar kungiyar kasuwanci mafi girma ta Afrika ta bayyana cewa, tana kyakkyawan fatan za'a gudanar da zaben kasar Kenya na ranar 8 ga watan Augusta cikin lumana.

Kungiyar 'yan kasuwa ta gabashi da kudancin Afrika wato (COMESA), ta bayyana cewa dukkan masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar sun bukaci magoya bayansu da su zauna lafiya.

Shugaban COMESA mai sa ido a zaben, Simbi Mubako, ya shedawa 'yan jaridu a Nairobi a lokacin da suka kaddamar da tura tawagoginsu zuwa sassan kasar dabam dabam cewa, suna da kyakkyawan tsammani zaben na Kenya zai gudana lami lafiya bisa la'akari da yadda masu ruwa da tsaki suka jajurce.

Tawagar masu sa idon, wanda ta isa kasar tun a ranar 30 ga watan Yuli, za ta ziyarci yankuna 29 na kasar domin sanya ido game da yadda za a gudanar da harkokin zaben.

Mubako ya ce, tawagarsa za ta ci gaba da zama a Kenya har zuwa ranar 10 ga watan Augasta, kuma za ta bayyana rahotannin farko da aka samu dangane da zaben.

Ya kara da cewa, alal hakika zaben da aka gudanar a kasar ta Kenya a shekarar 2013, an yi shi cikin kwanciyar hankali, hakan a cewarsa alamu ne dake nuna ci gaban da kasar ta samu ta fuskar ci gaban tsarin demokaradiyya.

Ya ce wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben ba a wancan lokacin, sun kalubalanci sakamakon zaben ne ta hanyar gabatar da korafe korafensu a gaban kotu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China