Tanzaniya ta sake musanta ta sa hannu cikin harkokin zaben kasar Kenya wanda za a gudanar a ranar 8 ga watan Augusta mai zuwa.
Ministar harkokin wajen kasar Augustine Mahiga, ta ce rahotanni da wasu kafafen yada labarai na Kenya suka ruwaito dake cewa Tanzania tana shiga harkokin zaben kasarsu, ba su da tushe bare makama.
Yayin wani taron manema labarai da aka yi a Dar es Salaam, babban birnin hada-hadar kasuwanci ta kasar, Augustine Mahiga, ta ce Tanzaniya ba ta taba ba, kuma ba za ta sa hannu cikin harkokin zaben kasashen waje ba, ciki kuwa, har da zaben kasar Kenya. (Fa'iza Mustapha)