in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun AU sun kwace wani yanki a kudancin Somaliya
2017-08-09 10:53:42 cri

Rundunar kungiyar tarayya Afrika dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya AMISOM, ta bayyana cewa dakarunta sun yi aiki na hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya SNA, inda suka ceto yankin Caalfodheere dake kudancin kasar ta Somaliya.

AMISOM ta ce, dakarun hadin gwiwar sun gudanar da aikin ne kusan kilomita 20 dake wajen garin Mahaday a Middle Shabelle, da nufin kwato hanyar da ke tsakanin Mahaday da Ceelbaraf, wadda ita ce babbar hanyar da fararen hula ke bi domin yin zirga-zirgarsu.

An ba da rahoton cewa, mayakan Al-Shabaab sun kaddamar da hari kan wata bataliyar sojoji mallakar rundunar ta AU, a kusa da garin Mahaday dake kudanci a ranar Litinin.

Wannan hari dai ya shafi wasu abubuwan fashewa ne wanda aka harba kan dakarun na AMISOM, daga bisani aka samu musayar wuta tsakanin mayakan da kuma dakarun sojin na AU a wajen garin.

Dakarun tsaro sun yi nasarar bude hanyoyin da mayakan suka toshe, lamarin da ya samar da wanzuwar tsaro a wannan yanki, inda al'ummar Somaliya suka ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China