in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Somliya ta fara shirin tantance mayakan A-Shabaab da suka mika wuya
2017-07-07 09:01:59 cri
Hukumomin tsaro a kasar Somaliya sun kaddamar da wasu matakan tantance mayakan Al-Shabaab da suka tuba da nufin komawa cikin al'umma.

Kwamandan hukumar tsaro da leken asiri na kasar Somaliya (NISA) mai kula da shirin tantance mayakan da suka tuba Abdifatah Sayid Ahmed ya ce shirin horas da tsoffin mayakan ya kunshi matakan tunkarar hadurra a lokacin tantancewar don gano wadanda ba su da wata mummunar illa ga al'umma. Kasashen Austria da Netherlands da Najeriya da Burtaniya sun yi amfani da wannan tsari.

A jiya ne dai aka kammala bitar matakan aiwatar da shirin na kwanaki biyu wanda ya samu goyon bayan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Somaliya (UNISOM) da kuma inganta kwarewar hukumar tsaron da leken asiri ta kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China