in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP ya karbi tallafin shinkafa wanda kasar Sin ta tallafawa Somaliya
2017-08-02 10:32:47 cri

Shirin samar da abinci na MDD wato (WFP) ya gudanar da bikin mika kayan tallafin shinkafa sama da ton 2,800 wanda kasar Sin ta tallafawa kasar Somali a babban birnin kasar Mogadishu sakamakon bala'in fari da ya afka wa kasar.

A cewar wata sanarwa da WFP ya fitar, ya bayyna cewa, tallafin da kasar Sin ta bayar zai baiwa WFP damar cigaba da ayyukansa na ceto rayukan mutane da kuma kawar da matsananciyar yunwa ga jama'ar kasar Somalia, sanarwa ta kara da cewa, WFP zai yi amfani da wannan tallafin wajen samar da abinci ga mutane marasa galihu kimanin 96,500 har na tsawon watanni 3.

Mataimakin daraktan shirin WFP a kasar Somaliya Edith Heines, ya bayyana cewa, shinkafar na daya daga cikin tallafin jin kai na dalar Amurka miliyan 10 wanda kasar Sin ta baiwa WFP daga watan Afrilun wannan shekara.

Qin Jian, jakadan kasar Sin a Somalia, ya bayyana a lokacin bikin cewa kasar Sin tana tallafawa Somaliya sakamakon ibtila'in fari da ya afkawa kasar Somaliyan. Ya ce baya ga tallafin abinci na dala miliyan 10 da kasar Sin ta bayar, haka kuma, kasar Sin ta samar da kayayyakin bada kulawar gaggawa da suka hada magunguna, da sinadarai masu gina jiki, da tanti da tankokin ruwa, ga mutanen dake cikin bukata a Somaliya, wannan ya nuna irin kyakkyawar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.

Maryan Quasim, ministar mai kula da al'amurran jin kai da kula da faruwar annoba a Somalia, ta bayyana cewa, gwamnatin Somaliya tana matukar farin cikin da irin wannan taimako da kasar Sin ta bayar, ta kara da cewa wannan ne karon farko da kasar Sin ta aike da tallafi ga kasar Somaliya a daidai lokacin da kasar ke cikin matsanancin hali. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China