in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi tir da harin da aka kai wa fararen hula a Mogadishu
2017-06-16 09:24:45 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da aka kai kan fararen hula da ke bude baki a ranar Laraba da daddare, a Mogadishu babban birnin Somalia.

Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar jiya, ta ruwaito Antonio Guterres na kuma yabawa da martanin gaggawa da jami'an tsaron kasar suka kai

Sakatare Janar din ya ce MDD, ba za ta taba kaucewa daga ci gaba da bada goyon baya ga al'umma da gwamnatin Somalia ba, a lokacin da suke tsaka da aiki tare domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

A ranar Laraba da dadddare ne wasu 'yan bindiga suka farwa gidajen abinci biyu a birnin Mogadishu, inda suka kashe mutane a kalla 17 da raunata wasu 26 tare kuma da yin garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China