Kakakin hukumar kiyaye tsaro na kasar shi ne ya bayyana hakan ga 'yan jarida yau. Ya kuma bayyana cewa, game da wadanda aka yi garkuwa da su a sakamakon harin, har yanzu ba a san yawansu da suka mutu ko suka raunata ba.
Rundunar 'yan sandan kasar Somaliya ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu harin boma-boman da aka kai a babban birnin kasar, Mogadishu ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda 18 tare da raunata mutane 19.
Kungiyar Al Shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari. (Zainab)