in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 15 ne suka rasu sakamakon wata fashewa a Somaliya
2017-06-20 20:23:19 cri
Ma'aikatar tsaron cikin gida ta kasar Somaliya ta ce a kalla mutane 15 sun rasa rayukansu, wasu da dama kuma sun jikkata, sakamakon wata fashewar wasu abubuwa a cikin wata mota, a gundumar Wadajir dake birnin Mogadishu na kasar Samaliya.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin ma'aikatar Ahmed Mohamed Mohamud, ya ce adadin wadanda harin ya hallaka na iya karuwa, duba da yadda wasu da suka ji raunuka sakamakon fashewar ta yau Talata ke cikin matsanancin yanayi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China