Taron wanda ake fatar shirya shi tsakanin ranar 10 zuwa 12 ga wannan watan a Nairobin kasar Kenya, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar NIEC ce za ta shirya da hadin gwiwar hukumar Arab EMBs, tare da tallafin hukumar inganta sha'anin zabe ta MDD IESG.
Wata sanarwa daga shirin raya ci gaban kasashe na MDD a Somali UNDP, ya bayyana cewa, wakilan za su tattauna batutuwa da suka shafi yin rajistar jam'iyyun siyasa, da duba hanyoyi da matakan da za'a yi amfani da su, da kuma yin musayar ilmi tsakanin kasashen Afrika da na Larabawa wadanda suka gudanar da makamancin wannan tsarin.
Sanarwar ta kara da cewa, ana fatar wannan babban taro zai taimakawa hukumar zaben kasar Somaliya wajen samun nasarar yin rajistar jam'iyyun siyasar kasar a kokarin tabbatar da tsarin na kowane mutum ya kada kuri'a guda a zaben kasar na shekarar 2020 da ta 2021. (Ahmad Fagam)