in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An kara yawan jiragen saman yaki da Boko Haram
2017-08-09 09:47:31 cri

A Najeriya an kaddamar da karin wasu jiragen sama na yaki guda 5, domin karfafa yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Yayin wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar na kaddamar da jiragen samfurin Mushshak jiya a jihar Kaduna dake arewacin kasar, mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya ce matakin sanya wadannan jirage cikin ayyukan yaki da Boko Haram a yanzu, ya zo daidai lokaci mafi dacewa. Mr. Osinbajo ya kara da cewa, dukkanin hare-hare da kungiyar ke kaddamarwa a yanzu, alamu ne na karaya, kuma nan gaba kadan za a kawo karshensu baki daya.

Gabanin hakan, cikin jawabinsa babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce komawar manyan dakarun rundunonin sojin kasar birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, ya taimaka wajen tattara bayanan da ake bukata, tare da daukar sahihan matakai, na kakkabe yankin daga gyauron mayakan na Boko Haram.

Air Marshal Abubakar, ya ce a kullum jiragen saman rundunarsa na sintiri na a kalla sa'oi 9 a yankunan dake kewaye da birnin Maiduguri, domin tabbatar da kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu. Ya ce yanzu haka sojin saman kasar na da jiragen yaki 10, yayin da suke fatan sanya karin wasu 5 a aikin da suke gudanarwa nan da watan Disamba mai zuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China