in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukunta na nuna damuwa game da yadda ake farwa jami'an tsaro a Najeriya
2017-08-08 09:24:29 cri
Mai rikon mukamin sakataren gwamnatin Najeriya Habitat Lawal, ta nuna damuwa game da yadda ake far wa jami'an tsaro a wasu sassan kasar, tana mai cewa yin hakan ya sabawa doka, kuma yana da matukar hadari ga zaman lafiya da walwalar al'ummar kasar.

Uwar gida Habitat ta ce ko alama gwamnati ba za ta kyale al'umma su ci gaba da gallazawa jami'an tsaro ba, duba da cewa a wasu lokutan hakan kan kai ga kisa ko garkuwa da jami'an tsaro, musamman ma jami'an hukumar kare hadurra ta kasar FRSC.

Ta ce dorewar hakan na iya zama barazana ga ayyukan jami'an tsaro, musamman ganin yadda a watan Yulin da ya gabata kadai, aka samu aukuwar irin wadannan hare hare har sau 10, ciki hadda harbin wasu jami'an hukumar ta FRSC da wasu 'yan sanda masu tsaron lafiyar kakakin majalisun dokokin jihar Abia suka yi a birnin Aba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China