in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hafsan sojojin Najeriya ya bukaci dakarun kasar su bankado maboyar yan ta'adda
2017-08-09 09:25:40 cri
Shugaban sojojin kasa na Najeriya Laftanal kanal Tukur Buratai, ya umarci sojojin kasar dasu kara kutsawa cikin dazuka domin bankado dukkan maboyar 'yan ta'adda na Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Buratai, ya ba da wannan umarni ne a garin Bama dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, bayan ba da lambar yabo da karin girma ga manyan jami'an sojojin kasar biyu, da kuma wasu kananan sojoji 63, sakamakon irin jajurcewar da suka nuna a cigaba da aikin da suke na fatattakan 'yan ta'adda.

Hafsan sojin ya bukaci dakarun sojin kasar da su ninka kokarin da suke yi domin cimma burin da aka sanya gaba, kana ya yi alkawarin ci gaba da kula da hakkoki da kuma jin dadin rayuwar sojojin Najeriyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China