in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta lashi takobin cafke wadanda ke da hannu kan kisan kiyashin da aka yi a wata Mujami'a
2017-08-08 09:10:49 cri
Gwamnatin Nijeriya ta lashi takobin cafkewa tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe masu ibada ranar Lahadin da ta gabata, a Mujami'ar darikar katolika ta St. Philips dake jihar Anambra, a kudu maso gabashin kasar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Abdurrahman Dambazau, wanda ya dauki alkawarin a jiya, cikin wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya yi tir da kakkausar murya, kan kisan, yana mai tabbatar da cewa za a dukufa wajen ganin wadanda ke da hannu sun fuskanci shari'a.

Abdurrahman Dambazau, ya kuma jajantawa al'ummar Ozubulu, da kuma iyalan wadanda aka kashe, da wadanda suka raunana da kuma kafatanin al'ummar jihar Anambra.

Ya bayyana al'amarin a matsayin na mugunta da tsoro, wanda ya ce 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro na gudanar da bincike a kai.

Da safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka farwa wata mujami'a a jihar Anambra, al'amarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan kasar su ma sun yi tir da harin, suna masu bayyana shi a matsayin laifin da ya sabawa hakkin dan Adam. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China