Wasu 'yan kunar bakin wake 3 da suka yi yunkurin tada boma bomai a birnin Maiduguri ranar Jumma'ar da ta gabata sun gamu da ajalinsu.
Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Borno Victor Isuzu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ya ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 da mintoci 49 na dare, a lokacin da maharan suka yi yunkurin kaddamar da hare-haren kunar bakin wake, wadanda suka hada da namiji daya da kuma mata biyu, maharan dai sun yi kokarin shiga yankin Usmanti dake birnin na Maiduguri.
Vintor ya ce jami'an tsaro ne suka dakile maharan a lokacin da suke yunkurin kaddamar da hare-hare, kuma har ma sun yi yunkurin tserewa, inda nan take abubuwan fashewar dake daure a jikinsu ya tashi da su ya hallakasu nan take.
Ya kara da cewa, biyu daga cikin jami'an tsaron sun samu raunuka, inda aka garzaya da su asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri don duba lafiyarsu.
Birnin Maiduguri da sauran yankunan da aka kwato su daga hannun 'yan ta'adda, suna fama da hare-haren kunar bakin wake, lamarin da ya haddasa hasarar rayuwa masu yawa da dukiyoyi, musamman cikin watanni biyun da suka gabata.
A kwanan baya ma, sai da 'yan tada kayar bayan suka kaddamar da hare hare kan tawagar jami'an dake gudanar da aikin binciken danyen mai a tafkin Chadi.
Haka zalika 'yan tada kayar sun kaddamar da hare-hare kan sansanin 'yan gudun hijira dake Maiduguri da yankin Dikwa a jahar ta Borno.(Ahmad Fagam)