Cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, ministan ya ce za a hade tsarin da sa manufofin ci gaban kasar, ta yadda zai zamo daya daga ginshikan da za su zaburar ta tattalin arzikin kasar nan da 'yan shekaru masu zuwa.
Mr. Onu ya kara da cewa, matakin zai ba da damar cin karin gajiya daga dimbin albarkatun kasa da Najeriya ke da su, da samar da karin guraben ayyukan yi, da rage fatara. Sauran sun hada da karfafawa matasan kasar gwiwar shiga fannonin kimiyya da fasaha, da rage yawan dogaro kan hajojin da ake shiga da su cikin kasar daga ketare.
Kaza lika a cewarsa hakan zai zaburar da tunanin masana a fannoni da dama, ta yadda za su ba da gudummawar da ta dace wajen fadada bangarorin kirkire-kirkire, da raya sha'anin kimiyya yadda ya kamata. (Saminu Hassan)