Gwamnan ya shaidawa karamar ministar kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed dake ziyara a jihar cewa, matsananciyar fatara da rashin ilimi ya sa matasa da dama shiga kungiyoyin 'yan ta'adda dake jefa al'umma cikin mawuyacin hali, musamman a yankin arewa maso gabas.
Abubakar Mohammed wanda ya bayyana haka a jiya, ya ce muddin ba a dauki matakin magance batutuwan ba, matsalar za ta ci gaba da ta'azzara.
Game da 'yan gudun hijira dake samun mafaka a jihar yanzu haka, Gwamnan ya ce jihar ba ta da sansanonin 'yan gudun hijira na din-din-din.
Har ila yau, gwamnan ya fadawa ministar cewa, yanzu 'yan gudun hijira na samun mafaka ne a wajen al'umma.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayyar kasar bisa taimakon kayayyakin jin kai da ta ba 'yan gudun hijirar dake jihar. (Fa'iza Mustapha)