in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake bukatar dakatar da jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD
2017-03-29 20:05:23 cri

A Larabar nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce har kullum kasar Sin na adawa da matakin kafa tsarin na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD a yankin da Sin take ciki da kasar Amurka ta dauka, don haka ta sake nanata bukatar a maida hankali da kulawar da take nunawa tare da sauran kasashen da ke yankin. Kaza lika Sin na fatan za a yi la'akari da babbar moriyarsa, a kuma dakatar da jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD.

A ranar 28 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya ce, Rasha da Sin na adawa da jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD wanda Amurka ke jagoranta, matakin zai kawo illa ga tsaron yankin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China