in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a hana yunkurin raya makaman nukiliya tare da gaggauta farfado da shawarwari kan batun Koriya ta Arewa, in ji ministan harkokin wajen Sin
2017-08-06 13:46:12 cri
Yayin da yake halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen gabashin Asiya wanda aka yi yau Lahadi a birnin Manila na kasar Philippines, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya amsa tambayoyin da 'yan jaridu suka yi masa, dangane da sabon kudirin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartas wanda ya jibanci kasar Koriya ta Arewa.

Wang Yi ya ce, da sanyin safiyar yau Lahadi, kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani sabon kudiri wanda ya shafi batun nukiliyar zirin Koriya. A matsayinta na kasa mai wakilicin dindindin a kwamitin sulhun MDD, Sin tana taka rawar a-zo-a-gani wajen warware matsalar nukiliyar Koriya ta Arewa.

Wang ya ce, wannan sabon kudiri na kunshe da manyan fannoni biyu. Na farko, kwamitin sulhun ya maida martani game da harba makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta rika yi, ta yadda za'a dauki matakai na hana duk wani yunkuri na Koriya ta Arewar na raya makaman nukiliyarta. Na biyu shi ne, a yi kira da a farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida, da warware batun nukiliyar zirin Koriya ta hanyar lumana da siyasa, domin kaucewa tabarbarewar halin da ake ciki a yankin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China