in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a karfafa ayyuka guda biyu don warware matsalar nukiliya ta Koriya ta Arewa
2017-06-03 13:07:01 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas game da batun kasar Koriya ta Arewa. Kana a gaggauta daukar matakan warware batun nukiliyar zirin Koriya cikin zaman lafiya, ta hanyar karfafa ayyuka guda biyu da za su hada da hana yaduwar makaman nukiliya da kuma inganta shawarwarin neman sulhu a tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, inda ya yi allah wadai da kakkausar murya kan gwajin makamai masu linzami da kasar Koriya ta Arewa ta yi, sa'an nan, an shigar da karin mutane da kamfanonin da abin ya shafa cikin jerin wadanda za a kakaba musu takunkumi.

A yayin taron, Liu Jieyi ya ce, ana fuskantar matsaloli da dama game da yanayin zirin Koriya, kuma a halin yanzu, ana cikin wani muhimmin lokaci ganin bangarorin daban daban da batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa ya shafa teburin sun koma ga yin shawarwari.

Bugu da kari, ya ce, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su kai zuciya nesa, domin sassauta yanayin tashin hankali da ake ciki, lamarin da zai ba da gudummawa wajen karfafa fahimtar juna a tsakaninsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China