in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha sun fidda wata sanarwa game da batun zirin Koriya
2017-07-05 15:55:42 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa da ta bayyana matsayar da suka cimma kan batun zirin Koriya.

Sanarwar da Ministocin biyu suka fitar a jiya, ta bayyana cewa, a wannan rana, kasar Koriya ta Arewa ta sanar da yin wani gwaji na harba makami mai linzami, lamarin da suka ce ya saba wa kudurin kwamitin sulhu na MDD.

Har ila yau, kasashen Sin da Rasha sun yi Allah wadai da wannan gwajin da Koriya ta Arewa ta yi, inda suka bukaci kasar da ta yi biyayya ga kudurin kwamitin sulhu na MDD yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China