in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Arewa ta sanar da harbar makami mai linzami mai karfin kai wa wata nahiya karo na biyu cikin nasara
2017-07-29 13:35:24 cri
Kasar Koriya ta Arewa ta sanar a yau cewa, ta cimma nasarar harbar makami mai linzami samfurin Hwasong-14 mai nisan zangon da ke da karfin kaiwa wata nahiya a daren jiya Jumma'a.

Rahoton kamfanin dillancin labaru na KCNA ya ruwaito a yau Asabar cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya sa hannu kan umurnin harbar makamin mai linzami karo na biyu, kana ya je wurin don gane wa idonsa harbin makamin a jiya.

Har ila yau, rahoton ya ce Kim Jong Un, ya bayyana cewa, harbar makamin ya shaida tabbacin tsarin makamai masu linzami da ke da karfin kai wa wata nahiya, baya ga nuna karfin kasar Koriya ta Arewa, na iya harbar makamai masu linzami a ko wane wuri da ko wane lokaci. Lamarin kuma ya nuna cewa, Amurka tana cikin zangon da irin makaman za su isa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China