in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce zai fi so a warware rikicin zirin Korea ta hanyar Diflomasiyya
2017-04-28 15:04:39 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai fi so a yi amfani da hanyar diflomasiyya wajen warware batun zirin Koriya, sai dai, ya yi gargadin cewa, za a iya fuskantar gagarumin rikici da Jamhuriyar Demokradiyyar Al'ummar Koriya.

Donald Trump ya fada yayin zantawa da kafar yada labarai ta Reuters a jiya Alhamis cewa, za su so a warware batutuwa ta hanyar diflomasiyya, sai dai abun da kamar wuya, yana mai cewa, akwai yiwuwar batun zai kai ga gagarumar rigima da Koriya ta arewa.

A ranar Laraba da ta gabata ne, manyan Jami'an Gwamnatin Trump, suka yi wa majalisar dokokin Amurka bayani dangane da manufar Washington a kan Koriya ta arewa.

Wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taro da 'ya'yan majalisar, ta ce Trump na da nufin amfani da takunkumin tattalin arziki da matakan diflomasiyya wajen matsawa Koriya ta arewa lamba, ta tarwatsa shirinta na makaman nukiliya da makamai masu linzami. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China