in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi allah wadai da gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ke yi
2017-07-05 10:53:40 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya yi allah wadai da gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi a jiya, yana mai bukatar kasar ta tsayar da gwajin nan take.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar a jiya Talata.

Rahotanni na cewa, Koriya ta Arewa, ta sanar a jiya cewa, ta cimma nasarar gwajin harba makami mai linzami na MARS-14.

A ranar 3 ga wata ne shugaban kasar Kim Jong-un, ya sanya hannu kan umurnin harba makamin, inda a jiya kuma, ya je wurin da aka harbe shi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China