Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta jaddada a nan Beijing cewa, kasar Sin ba za ta sauya matsayinta dangane da batun nukiliyar zirin Koriya, da kuma batun shirin jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD ba. Kana har yanzu ba ta rama matakin da kasar Koriya ta Kudun ta dauka ba.
Madam Hua ta fadi hakan ne, dangane da daftarin shirin da wasu 'yan majalisar kasar Amurka suka gabatar, inda suka ce, kasar Sin tana ramuwar gayya kan Koriya ta Kudu, sakamakon jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD. (Tasallah Yuan)