in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin ya fara gina tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa a Angola
2017-08-05 13:29:27 cri
An yi bikin kaddamar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki daga karfin ruwa ta Caculo Cabaca a birnin Dundo dake lardin Kuanza Norte na kasar Angola a jiya Jumma'a, inda ya samu halartar shugaban kasar Jose Eduardo Dos Santos.

Rahotanni na cewa, tashar samar da wutar lantarki mai aiki da karfin ruwa da kamfanin kasar Sin zai gina a kasar Angola, za ta kasance tashar lantarki mafi girma da kamfanin kasar Sin ya taba ginawa a duk fadin nahiyar Afirka.

Mataimakin manajan kamfanin Gezhouba, da ya dauki nauyin gina tashar Ren Jianguo, ya yi bayani cewa, aikin gina tashar Caculo Cabaca zai lakume dallar Amurka miliyan 4532, kuma bisa yadda aka tsara, za a kammala ta cikin watanni 80 masu zuwa, inda zai samar da guraben ayyukan yi kusan dubu goma ga mazauna yankin.

Haka zalika, bayan kammala ginin tashar, adadin wutar lantarki da tashar za ta samar zai biyan bukatun al'ummomi sama da kashi 50 bisa dari, yayin da zai ba da gudummawa matuka wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasar.

A nasa jawabin, Ministan kula da harkokin makamashi da albarkatun ruwa na kasar Angola Joao Baptista Borges, ya bayyana cewa, a matsayinta na tashar samar da wutar lantarki daga karfin ruwa mafi girma da ake ginawa a Angola, tashar Caculo Cabaca na da muhimmanci wajen raya tattalin arzikin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China