Gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin bai wa gwamnatin kasar Angola kyautar kudi na dalar Amurka dubu 500 cikin gaggawa, a kokarin taimakawa jama'ar kasar sayen allurar rigakafin zazzabin shawara domin yaki da cutar cikin hanzari.
Wakilinmu ya samu wannan labari ne yau Jumma'a 5 ga wata daga ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin.
An ba da labarin cewa, ya zuwa karshen shekarar bara ta 2015, zazzabin shawara ta kama wasu mutane tare da halaka wasu a birnin Viana da ke lardin Luanda na Angola. Da zummar hana yaduwar cutar, gwamnatin Angola ta roki kasar Sin ta ba da taimakon gaggawa. (Tasallah Yuan)