in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Angola na daukar matakai na kare muhalli
2016-06-06 09:39:14 cri
Mataimakin shugaban kasar Angola Manuel Vincente, ya jaddada kudurin kasar sa na tabbatar da kare muhallin halittu da ma nau'oin halittu daban daban, musamman ma irin wadanda ake samun su a kasar ta Angola kadai.

Mr. Vincent wanda ke jawabi a madadin shugaban kasar ta Angola Jose Eduardo Dos Santos, yayin taron ranar 5 ga wata, na ranar muhalli ta duniya wanda babban daraktan hukumar UNEP ta MDD Achim Stainer ya halarta, ya kara da cewa karkashin wannan manufa, mahukuntan Angola na bada kulawa matuka ga kare dabbobi, da tsirran dake fuskantar barazanar bacewa daga ban kasa.

Dan gane da hakan ne ma Mr. Vincent ya bukaci karin hadin gwiwa daga masu ruwa da tsaki na shiyya shiyya, da na kasa da kasa, wajen dakile laifukan dake da alaka da keta dokokin kare muhallin halittu, da nau'oin halittun dake rayuwa a doron kasa, musamman duba da irin kalubale da duniya take fuskanta wajen aiwatar da hakan.

Ya ce ya zama wajibi a tashi tsaye, wajen yakar masu farauta, da masu fataucin albarkatun daji, ciki hadda dabbobi ba bisa ka'ida ba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China