in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: Cutar zazzabin shawara a Angola ta sami sassauci
2016-08-07 14:05:35 cri
A jiya Asabar, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ba da rahoton cewa, an samu saukin yaduwar cutar zazzabin shawara da ta barke a kasar Angola tun a watannin shidan farko na wannan shekara, hukumar tace cikin makwanni shida da suka wuce, ba'a samu karin wadanda suka kamu da cutar ba a kasar.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, a karshen watan Janairun bana, an samu wanda ya kamu da cutar zazzabin shawara na farko a kasar Angola. Ya zuwa karshen watan Yuli kuma, baki daya an nuna tababa ga mutane 3818 da ake zaton sun kamu da cutar a kasar, a ciki an tabbatar da wadanda suka kamu da cutar 879, yayin da mutane 369 suka mutu sakamakon haka. A kasar Kongo Kinshasa dake makwabtaka, ya zuwa karshen watan Yuli, ana tababa game da mutane 2051 da ake zargin sun kamu da cutar ta zazzabin shawara, sai dai daga cikin wannan adadin mutane 76 ne aka hakikance sun kamu da cutar, yayin da wasu 95 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

A karkashin hadin gwiwa tsakanin kungiyar da ke kula da aikin ajiye allurar yaki da cutar zazzabi cikin gaggawa, da hadaddiyar kungiyar hadin gwiwa ta rigakafin cututtuka ta duniya, da kamfanonin samar da alluran rigakafin cututtuka da sauransu, ya zuwa yanzu, jama'ar Angola da Kongo Kinshasa sama da miliyan 16 sun samu alluran rigakafin yaki da cutar zazzabin. Kafin shigowar yanayin damina a watan Satumban bana, an kiyasta cewa, karin mutane miliyan 17 za su samu alluran rigakafin cutar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China