Manuel Vicete ya yi wannan jawabi ne jiya a birnin Luanda, lokacin da yake ganawa da dan majalisar gudanarwar Sin kuma Ministan tsaron kasar Chang Wanquan dake ziyara a kasar.
Mataimakin shugaban kasar ya ce kasashen biyu na amfana da ingantaccen tubalin dangantaka dake tsakaninsu, wanda ya ce yana da muhimmanci wajen dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Ya ce Angola ta dauki shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta gabatar da matukar daraja, kuma a shirye take ta hada hannu da kasar karkashin shirin, domin samun ci gaba na bai daya ta yadda al'ummomin kasashen biyu za su amfana.
A nasa bangaren, Chang Wanquan ya ce makasudin ziyarar ta sa shi ne, aiwatar da muhimmin mataki da shugabannin kasashen biyu suka cimma, domin inganta hadin kai a dukkan bangarori, ciki har da tsaro, tare da daukaka huldar dake tsakaninsu zuwa wani mataki. (Fa'iza Mustapha)