A ranar laraban nan, ake sa ran kwamitin sulhun ta amince da shawarar garkama takunkumi akan kasar Korea ta arewa domin dakile shirin ta na Nukuliya . MDD ta rarraba takardar kudurin ga kwamitin mai mambobi 15 a makon jiya.
A karkashin kudurin, kwamitin sulhun tana da cikakken iko na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.
Kwamitin yana kunshe da mambobin kasashen dindindin da suka hada da kasashen Sin, Amurka,Britaniya,Faransa da kuma Rasha, sannan akwai kasashe 10 da ba na dindindin ba da aka zaba cikin rukunai biyar da suke jagoranci na shekaru biyu biyu a kwamitin.
Shugabancin kwamitin ana karba karba ne tsakanin kasashe mambobi 15 da suke jeri bisa haruffan Turanci a duk wata.(Fatimah Jibril)