in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude reshen Bank of China a kasar Angola
2017-06-06 09:36:46 cri
A jiya Litinin ne bankin kasar Sin wato Bank of China a Turance ya bude reshensa a Luanda, babban birnin kasar Angola. Kuma shi ne bankin kasar Sin na farko da aka bude a kasar ta Angola.

Da yake karin haske yayin bikin bude reshen bankin, shugaban bankin Chen Siqing, ya bayyana cewa, reshen bankin zai mayar da hankalinsa ne kan harkokin kamfanoni da hidimomin da suka shafi samar da rance, ajiyar kudade, daidaita harkokin kudade na kasa da kasa, cinikayya, kasuwannin kudade da sauransu. Ana kuma sa ran bankin zai shiga a dama da shi wajen samarwa kamfanoni da abokan hulda kudaden tafiyar da harkokin kasuwanci tsakanin kasashe.

Chen ya kara da cewa, kasashen biyu suna da kudurin raya kasa da gina ginshikin hadin gwiwar moriyar juna. A shekarar 2016 an yi kiyasin cewa, cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 15.6.

A halin da ake ciki kuma, bankin zai taimakawa kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Angola, da kuma kamfanonin Angola su bunkasa kasuwannin kasar Sin ta yadda za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin sun hada da wakilai na bangarorin siyasa, tattalin arziki da harkokin kudi kimanin 300 daga kasashen biyu. A yau ne ake sa ran reshen bankin zai fara aiki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China