Sanarwar da hedkwatar dakarun hadin gwiwa da aka kafa a kasar Iraq ta fitar jiya ta ce, bisa rahotannin da ta samu daga hukumar leken asiri na kasar, sojin saman Iraq sun kai hari kan sansanoni uku na mayakan kungiyar IS a birnin Ba'aj na yankin iyakar dake tsakanin kasar Iraq da Syria, inda suka halaka 'yan ta'adda sama da 150 da suka shiga kasar daga Syria.
A halin yanzu, kungiyar IS na ci gaba da rike da iko da birnin Ba'aj wanda yake da nisan kilomita 130 daga birnin Mosul na Iraq.
Birnin Ba'aj dai ya kasance wata muhimmiyar hanya ga mayakan IS wajen shiga da fita tsakanin kasar Iraqi da Syria.
A nasu bangare, sojojin gwamnatin kasar Iraq sun dukufa wajen kwace baki dayan binrin Mosul daga hannun kungiyar IS. (Maryam)