Kasar Sin ta ce ba za ta tsoma baki a harkokin cikin wata kasa ba. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang shi ne ya bayyana a yau lokacin da ya ambato batun tsige Park Geun-hye daga mukaminta na shugabar kasar Koriya ta Kudu a yayin taron manema labarai da aka shiryawa.
A matsayinta na makwabciyar Koriya ta Kudu, kasar Sin tana fatan samun kwanciyar hankali a harkokin siyasar Koriya ta Kudun.
Geng Shuang ya kuma sake yin kira ga Koriya ta Kudu da ta dakatar da shirin da ake na jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD, a kokarin kawar da duk wani shinge na maido da kyakkyawan bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen 2. (Tasallah Yuan)