Rahotanni na cewa ayyukan da za su shafi filayen jiragen sama 17 a jihar ta Xinjiang, za su bunkasa matsayin yankin na kasancewa wata cibiya, wadda za ta kara sada kasar Sin da sauran yankunan tsakiyar nahiyar Asiya.
Cikin filayen jiragen saman 17, 14 na sufurin fasinjoji ne, wadanda za a yi aikin su a biranen Urumqi, da Kashgar, da Aksu, da Yining, da Korla da Altay, da kuma wasu gundumomi da suka hada da Zhaosu, da Yutian da Shache. Sai kuma wasu falayen jiragen 3 na dakon kaya da fasinjoji.
Bisa tsarin ayyukan, za a fara ne da kammala filin jiragen saman Shache a wannan shekara da muke ciki. Filin da zai zamo na 19 a jihar ta Xinjiang.