in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Xinjiang ya gabatar da doka da ta zama ta farko a kasar Sin ta magance tsattsauran ra'ayin addini
2017-03-31 10:46:25 cri
Yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na Uygur dake arewa maso gabashin kasar Sin ya gabatar da wasu dokoki a karon farko ga kasar Sin, domin dakile tsattsauran ra'ayin addini, wadanda za su fara aiki a gobe Asabar.

Dokokin sun fayyace yadda ayyukan masu tsattsauran ra'ayin addini sukke, da kuma bayyana cikakkun matakai da za a bi domin dakilesu, kana an zayyana irin hakkoki da nauyin dake wuyan gwamnatoci da ma'aikata har da sauran al'umma ta yadda za'a magance wannan matsaloli.

A cewar wadannan dokoki, akwai abubuwa kimanin 15 da ake bayyana su a matsayin tsattsauran ra'ayin addini wadanda suka hada da: yin katsalandan game da 'yancin addinin wasu, tilastawa mutane shiga al'amurran addini, fitar da mabiya addinai daban daban daga gidajensu, halatta abubuwan da shara'a bata halatta ba wadanda basu shafi abinci ba, sanyawa ko kuma tilastawa wasu sanya nau'in suturu kamar irinsu burqa, yin aure ko kuma saki wanda ya sabawa shara'a, da hana yara kanana hakkinsu na ilmin kasa.

Shugaban makarantar koyon shari'a ta jami'ar Xinjiang Chen Tong, yace gabatar da dokoki a fayyace sune suke tabbatar da addinin gaskiya da na karya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China