Mr. Guterres ya ce, ana fatan bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da shawarwari tsakaninsu domin karfafa fahimtar juna. Kaza lika zai ci gaba da yin cudanya da bangarorin da abin ya shafa.
A ranar 14 ga watan nan da muke ciki ne, 'yan sandan Isra'ila guda biyu sun rasu sakamakon harin da aka kai musu a masallacin Kudus, bayan hakan ne kuma Isra'ila ta sa wata kofar binciken jikin masu shiga masallacin, lamarin da ya haddasa dauki ba dadi tsakanin Isra'ila da tsagin Falesdinawa, kuma ya zuwa yanzu, hakan ya haddasa rasuwar mutane 10, yayin da wasu kimanin 500 suka jikkata.
A ranar 25 ga wata, hukumar tsaron Isra'ila ta tsai da kudurin kau da wannan kofa ta bincike. Har wa yau a ranar 27 ga wata, limamin al'ummar musulmi a birnin na kudus Sheikh Muhamad Ahmad Hussein, ya sanar da kawo karshen tashin hankali tsakanin Isra'ila da Palasdinawa kan wannan batu. (Maryam)