in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya nuna rashin jin dadi game da barkewar rikici a tsohon birnin Jerusalem
2017-07-22 12:48:40 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa game da yanayin da ake ciki a tsohon birnin Jerusalam, inda rikici ke kara ta'azzara a baya-bayan nan tsakanin Isra'ilawa da Falasdinawa.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar jiya Juma'a, Antonio Guterres ya bayyana rashin jin dadi game da mutuwar Falasdinawa uku a rikicin da ya auku jiya da dakarun Isra'ila, ya na mai kira da a gudanar da cikakken bincike kan al'amarin.

Sakatare Janar din ya bukaci shugabannin Falasdinawa da na Isra'ila su kauracewa yin abubuwan da ka iya ta'azzara yanayin da ake ciki.

An samu sabani a gabashin Jerusalem da yammacin kogin Jordan a jiya Juma'a ne bayan Isra'ila ta takaita Musulmin da za su samu damar zuwa harabar masallacin Al-Aqsa dake tsohon birnin Jerusalam, inda ta ce mata da maza da suka haura shekaru 50 ne kadai za a bari shiga masallacin.

Jami'an Isra'ila sun ce wani bafalasdine dauke da wuka ya kashe isra'ilawa uku tare da raunata wani guda a yankin gabar yamma da kogin Jordan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China