in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila za ta cire na'urorin gano makamai daga wuraren shiga wajen ibada na Kudus
2017-07-25 10:51:53 cri

Biyo bayan rikicin da aka shafe kwanaki da dama ana yi, majalisar tsaron Isra'ila, ta yanke shawarar cire na'urorin gano makamai daga wuraren shiga wajen ibada mai tsarki na birnin Kudus da aka fi sani da masallaci mai daraja a tsakanin musulmai yayin da Yahudawa ke kiransa da Temple Mount.

Wata sanarwar da ofishin firaministan kasar ya fitar, ta ce majalisar tsaron ta amince da shawarar da dukkanin hukumomin tsaro suka ba da, wadda ta nemi a yi amfani da fasahohin tsaro na zamani da sauran matakai, maimakon na'urorin gano makamai, domin tabbatar da tsaron masu kai ziyara da masu ibada a tsohon birnin da wajen ibada mai tsarki.

Sanarwar ta kara da cewa, runduanr 'yan sandan Isra'ila za ta karfafa rundunoninta don kara daukar matakan da suka dace da nufin tabbatar da tsaron masu kai ziyara da wajen ibadar.

An sanar da wannan mataki ne bayan kammala taron majalisar tsaron da ya shafe sa'o'i da dama.

Na'urorin da aka girke bayan wani hari da ya kai ga kisan 'yan sandan Isra'ila uku, ya janyo gagarumar zanga-zanga.

Falasdinawa na ganin matakin a matsayin take musu hakkin da suke da shi kan harabar Ibadan da kuma yunkurin Isra'ila na samun karin iko da wajen. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China