Karkashin sabuwar dokar, wadda ta fara aiki tun a ranar 1 ga watan Mayu, dokar ta nemi ma'aikatan su ajiye kashi 20 cikin 100 na kudaden da suke samu a wani asusu na kasar. Kuma zasu iya samun kudaden da suka ajiye ne a lokacin da bakin masu neman mafakar zasu bar kasar Isra'ilan.
Ma'aikata 'yan cin ranin sun gudanar da zanga zangar ne tare da wasu 'yan asalin kasar Isra'ilan dake musu goyon baya, daga cikinsu akwai masu gidajen abinci, wadanda su ne mafi yawan ma'aikatan 'yan ciranin dake Tel Aviv ke musu aiki.
Wata kididdiga da mahukuntan kasar suka bayar ta nuna cewa, ya zuwa karshen watan Fabrairu, kimanin baki dubu 22 ne ke neman mafaka a Israilan. Kuma mafi yawansu sun zo ne daga kasashen Eritrea da Sudan.
Karkashin dokokin Israeli da na kasa da kasa, basu amince a tusa keyar masu neman mafakar zuwa kasashensu na ainihi ba, indan zasu iya fuskantar hukuncin kisa.(Ahmad Fagam)