Shugaban ya fadi haka ne a wajen taron manema labaru da aka kira bayan ganawar da ya yi tare da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, wanda ke ziyara a Palasdinu. A cewar Abbas, yayin da yake ganawa da shugaban kasar Amurka Donald Trump a birnin Washington, ya taba bayyana matsayin da ya dauka cewa, bisa yunkurin kasar Amurka na bude sabon zagayen shawarwari tsakanin Palasdinu da Isra'ila, shi da kansa a shirye yake ya gana da Benjamin Netanyahu, tare da yin hadin gwiwa da shi.
A nasa bangaren, Steinmeier ya ce, tabbatar da matsayin Palasdinu da Isra'ila a matsayin kasashe 2 masu ikon gashin kansu, ita ce hanya daya tilo da za ta tabbatar da warware rikicin dake tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)