Sanarwar ta bayyana cewa, kasashe mambobin kwamitin sulhun sun yi Allah wadai da dukkan hare-haren da aka kai wa tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Afirka ta Tsakiya, duk wane irin harin da aka kaiwa masu kiyaye zaman lafiyar ya zama laifin aikata yaki.
Kwamitin sulhun ya yi kira ga gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya da ta yi bincike kan wannan hari cikin hanzari, ta kuma gurfanar wadanda ke da hannu a kai harin a gaban kotu. Mambobin kwamitin sulhun sun jaddada cewa, sun nuna goyon baya ga tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Afirka ta Tsakiya da ta taimakawa kasar wajen sake shimfida zaman lafiya a kasar. (Zainab)