MDD ta yi marhabin da samun ci gaban yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar Afirka ta Tsakiya
A jiya Laraba 16 ga wata, kwamitin sulhun MDD ya zartas da sanarwar yin marhabin da samun ci gaban yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar Afirka ta Tsakiya, kuma ya yi kira da aiwatar da tsarin kawar da makamai da tsarin samun daidaito da aka daddale tun da wuri.
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasar Afirka ta Tsakiya tana cikin yanayin tangal tangal, yayin da fararen hula da yawa ke yin gudun hijira. Tun daga farkon bana zuwa yanzu, ana ta fama da matsalar rashin tsaro da rikice-rikice tsakanin kabilu da kai hari kan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya da sauransu a wasu wuraren dake kasar.(Fatima)