Game da hakan Mr. Dujarric ya bayyana cewa bisa rahotannin da aka samu, dakarun kungiyar Lord's Resistance Army (LRA) ne suka kaddamar da harin a wani kauye dake kusa da garin Rafaï, na lardin Mbomou dake Afirka ta Tsakiya, sai dai daga bisani an tura wata rundunar soja ta MDD dake kasar zuwa wannan kauye.
Stephane Dujarric ya kara da cewa, Ban Ki-moon ya jaddada cewa, ba za a kyale duk wani mataki na kaiwa ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, dake sadaukar da kansu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar Afirka ta Tsakiya ba. Ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar da ta dage wajen bankado tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kotu.
A wani ci gaban kuma, a jiya Litinin ne kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwar dake Allah wadai kan wannan danyen aiki, inda sanarwar ta bayyana cewa, mai yiwuwa ne irin wannan harin da aka kaddamar ya zama laifin yaki. Sanarwar ta kuma kalubalanci gwamnatin Afirka ta Tsakiya da ta cafke masu hannu cikin wannan ta'asa. (Fatima)