A jiya Lahadi ne mahukuntan kasar Isra'ila suka sake bude harabar masallacin Al Aqsa, bayan da 'yan sandan Isra'ilar suka hana musulmai yin sallar Jumma'a a masallacin, biyo bayan harbe wasu 'yan sandanta guda biyu da aka yi a kusa da masallacin, kamar yadda tashar Al-Arabiya dake watsa shirye-shiryenta da harshen Larabci ta bayyana.(Ibrahim)