in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su sake yin shawarwari cikin hanzari
2017-06-21 13:11:27 cri
A jiya Talata, zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi, ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su yi hakuri da juna da mayar da yin shawarwarin shimfida zaman lafiya don cimma shirin kasashen biyu cikin hanzari.

Liu Jieyi, ya yi jawabi a gun taron kwamitin sulhun MDD kan batun Palesdinu cewa, kafa kasar Palesdinu da samun zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila su ne aikin da kasa da kasa suke yin kokarin cimmawa. Kafa kasar Palesdinu mai cikakken ikon mallaka dake maida birnin Kudus ta gabas a matsayin babban birnin kasar da iyakar kasa da aka tsara a shekarar 1967 shi ne hakkin jama'ar Palesdinu, kana shi ne muhimmin batu don warware matsalar Palesdinu. Kamata ya yi bangarori daban daban su tsaya tsayin daka kan yunkurin shimfida zaman lafiya bisa tushen ka'idar yin amfani da yankin kasa don mayar da zaman lafiya, shirin kasashen biyu, kiran shimfida zaman lafiya na kasashen Larabawa, da kudurorin da kwamitin sulhun MDD suka zartas game da batun.

Liu Jieyi ya kara da cewsa, Sin ta nuna goyon baya ga sha'anin neman adalci na jama'ar Palesdinu, kana ita ce mai shiga-tsakani kan shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Ya ce, Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da bangarori daban daban wajen sa kaimi ga warware batun cikin adalci a dukkan fannoni cikin hanzari tare da samun zaman lafiya da na karko a yankin Gabas ta Tsakiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China