Bugu da kari, jiya Litinin, Xie Xiaoyan ya jaddada a yayin taron manema labarai da aka yi a birnin Ankara na kasar Turkiyya cewa, kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen inganta shawarwarin neman sulhu a tsakanin bangarorin da batun Syria ya shafa, domin neman ci gaba a fannoni guda hudu da suka hada da: tsagaita bude wuta, da gudanar da shawarwarin siyasa, da ba da taimakon jin kai, da kuma yaki da ta'addanci cikin hadin gwiwa.