Kungiyar SDF din mai kunshe da dakarun Kurdawa da Larabawa da sauransu tana kokarin kare yankunan dake karkashin kulawarta a wasu wuraren dake arewacin kasar Syria, bisa ga fadan da take yi da kungiyar IS. Kuma wata sabuwar nasarar da dakarun SDF suka samu ita ce, yadda suka samu nasarar mallakar karin ungwanni birnin Raqqa, wani garin dake arewacin kasar Syria, wanda ya kasance wata muhimmiyar mafaka ga kungiyar IS. Sai dai masu sa ido kan aikace-aikacen keta hakkin dan Adam a Syria sun ce, ko da yake dakarun SDF sun samu ci gaba a cikin birnin, amma har yanzu yake-yaken da suke yi tare da kungiyar IS ba su shiga cikin tsakiyar birnin ba tukuna.
Kungiyar SDF ta sanar da fara neman 'yantar da lardin Raqqa ne tun a ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2016. Zuwa watan Yunin bana, ta fara samun babban ci gaban a yakin da take yi da dakarun na IS.(Bello Wang)