in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD a kasar Syria ya kaddamar da sabon zagayen tattaunawar sulhun kan rikicin kasar
2017-07-11 10:39:05 cri

A ranar Litinin wakilin musamman na MDD a kasar Syria, Staffan de Mistura, ya jagoranci bude wani sabon zagaye na tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin Syriar da shugabannin 'yan adawar kasar, wanda ya bayyanata da cewa an shiryata ne da nufin saukaka hanyoyin da za'a samu maslahar kawo karshen yakin basasar kasar da ya shafe shekaru 7 ana gwambzawa.

De Mistura, ya shedawa 'yan jaridu jin kadan bayan kammala ganawa da wakilin gwamnatin Syria, inda jakadan Syria a MDD Bashar Jaafari ya wakilci gwamnatin, a lokacin tattaunawar.

Daga bisani a wannan ranar, ya bayyana cewa ya gana da wakilan shugabannin 'yan adawar kasar, da wakilan mambobin kasashe 5 na dindindin na MDD da suka hada da Kasar Sin, Faransa, Rasha, Amurka da Burtaniya, yana mai cewa, ya samu goyon baya mai matukar karfi.

An fara tattaunawar ce a birnin Geneva, karo na 7, biyowa bayan cikakkiyar tsakaita bude wuta ta wuni guda da aka samu a kudancin Syriar wanda kasashen Amurka, Rasha da Jordan suka jagoranta a makon jiya, da nufin samun kyakkyawan yanayin don tattaunawar sulhu da nufin kawo karshen rikicin kasar Syriar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China